Fári da Ƙarancin Ruwan Sama: Mene ne Ke Jawowa?
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
الحمد لله رب العالمين، والصلاة والسلام على سيدنا محمد، وعلى آله وصحبه أجمعين.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya ruwa a matsayin tushen rayuwa. Ya ce:
﴿وَجَعَلْنَا مِنَ الْمَاءِ كُلَّ شَيْءٍ حَيٍّ﴾
_”Kuma Mun sanya daga ruwa kowane abu mai rai.”_
(Suratul Anbiyā’: 30)
Saboda haka, idan aka samu ƙarancin ruwa ko ya ƙi dawwama, bai kamata mumini ya ɗauke shi a matsayin wani al’amari na yanayi kawai ba. Ya kamata ya tuna cewa komai yana ƙarƙashin ikon Allah.
Me ke jawo fári?
A cikin Alƙur’ani da Sunnah, an bayyana cewa wasu zunubai na iya zama sanadin hana albarkar sama da ƙasa.
Allah Ya ce:
﴿وَلَوْ أَنَّ أَهْلَ الْقُرَىٰ آمَنُوا وَاتَّقَوْا لَفَتَحْنَا عَلَيْهِم بَرَكَاتٍ مِنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ﴾
_”Da mutanen garuruwa sun yi imani kuma suka yi taƙawa, da Mun buɗe musu albarkatu daga sama da ƙasa.”_
(Suratul A’rāf: 96)
Wannan aya ta na nuna cewa imani da taƙawa su na jawo albarka, yayin da saɓo da zalunci su ke iya hana albarkar.
Haka nan Manzon Allah ﷺ ya ce:
«وَلَمْ يَمْنَعُوا زَكَاةَ أَمْوَالِهِمْ إِلَّا مُنِعُوا الْقَطْرَ مِنَ السَّمَاءِ، وَلَوْلَا الْبَهَائِمُ لَمْ يُمْطَرُوا»
_”Ba za su hana zakar dukiyoyinsu ba face an hana su ruwan sama. Kuma da ba domin dabbobi ba, da ba za a saukar musu da ruwan ba.”_
— رواه ابن ماجه وصححه الألباني.
Darussa:
Fári na iya zama:
Jarabawa daga Allah domin Ya gwada bayinsa.
Gargaɗi domin mutane su tuba daga zunubai.
Sakamakon yawaitar zalunci, cin hanci, karya amana, yanke zumunci, da sakaci da haƙƙoƙin Allah.
Don haka, abin farko da ya dace shi ne mu fara binciken kanmu, ba wai mu fara zargin yanayi ko gwamnati kawai ba.
Allah Ya ce:
﴿وَمَا أَصَابَكُمْ مِنْ مُصِيبَةٍ فَبِمَا كَسَبَتْ أَيْدِيكُمْ وَيَعْفُو عَنْ كَثِيرٍ﴾
_”Duk wata masifa da ta same ku, saboda abin da hannuwanku suka aikatawa ne, kuma Allah Yana yafewa da yawa.”_
(Suratush Shūrā: 30)
Tambihi:
Lokacin da aka ga alamun ƙarancin ruwa, bai kamata musulmi ya yanke ƙauna ba. Allah Shi ne Mai saukar da girgije, Mai rahama ga bayinsa, kuma Ya na amsa addu’ar masu nemanSa idan sun tuba suka koma gare Shi.
اللَّهُمَّ اسْقِنَا غَيْثًا مُغِيثًا، مَرِيئًا، مَرِيعًا، نَافِعًا غَيْرَ ضَارٍّ، عَاجِلًا غَيْرَ آجِلٍ.
_Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan rahama, mai wadatarwa, mai albarka, mai amfani ba mai cutarwa ba, cikin gaggawa ba tare da jinkiri ba._
…Za mu ci gaba In Sha Allahu.
Sa’id Husain Abdullahi
