By Sa’id Husain Abdullahi
Me Ya Kamata Bayin Allah Su Yi Idan Aka Samu Fári da Ƙarancin Ruwan Sama?
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
الحمد لله رب العالمين، والصلاة والسلام على سيدنا محمد، وعلى آله وصحبه أجمعين.
Bayan mun fahimci cewa dukkan al’amura suna ƙarƙashin ikon Allah Maɗaukakin Sarki, kuma fári na iya zama jarabawa ko gargaɗi, to abin da ya fi dacewa ga mumini shi ne ya koma ga Ubangijinsa da tawali’u da tuba.
1. Tuba na Gaskiya.
Abu na farko shi ne tuba daga dukkan zunubai, na fili da na ɓoye.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:
﴿فَقُلْتُ اسْتَغْفِرُوا رَبَّكُمْ إِنَّهُ كَانَ غَفَّارًا يُرْسِلِ السَّمَاءَ عَلَيْكُمْ مِدْرَارًا﴾
_”Sai na ce: Ku nemi gafarar Ubangijinku; lalle Shi Mai yawan gafara ne. Zai aiko muku da ruwan sama mai yawa.”_
(Suratu Nūḥ: 10–11)
Wannan aya ta nuna cewa yawaita istigfari na daga cikin manyan hanyoyin samun saukar ruwan sama.
2. Yawaita Istigfari da Addu’a.
Musulmi ya riƙa yawaita faɗin:
أَسْتَغْفِرُ اللَّهَ وَأَتُوبُ إِلَيْهِ
Kuma ya yawaita roƙon Allah Ya saukar da ruwan rahama.
Daga cikin addu’o’in da Manzon Allah ﷺ ya koyar akwai:
اللَّهُمَّ اسْقِنَا غَيْثًا مُغِيثًا، مَرِيئًا، مَرِيعًا، نَافِعًا غَيْرَ ضَارٍّ، عَاجِلًا غَيْرَ آجِلٍ.
_”Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan rahama mai wadatarwa, mai albarka, mai amfani ba mai cutarwa ba, cikin gaggawa ba tare da jinkiri ba.”_
3. Mayar da Haƙƙoƙin Jama’a.
Duk wanda ya ci amanar wani, ya zalunce shi ko ya karɓi haƙƙinsa, ya gaggauta mayar da shi ko neman yafiya.
Domin zalunci yana daga cikin manyan abubuwan da ke hana albarkar Allah.
4. Yawaita Sadaka.
Sadaka tana jawo rahamar Allah kuma tana kawar da bala’i da izninSa.
Saboda haka, a taimaki mabukata, marasa ƙarfi, marayu da zawarawa gwargwadon iko.
5. Gyara Mu’amala da Zumunci.
Yanke zumunci, ƙiyayya, hassada da gaba suna daga cikin abubuwan da ke hana albarka.
Ya dace ‘yan uwa, maƙwabta da abokan hulɗa su sasanta tsakaninsu, su yafe wa juna domin neman yardar Allah.
6. Yawaita Ayyukan Alheri.
A ƙarfafa:
– Tsayar da salla a kan lokaci.
– Karatun Alƙur’ani.
– Ambaton Allah (zikiri).
– Umurni da kyakkyawan aiki.
– Hana mummunan aiki cikin hikima.
Idan Har Ba a Samu Saukar Ruwan ba;
Idan aka ci gaba da fama da ƙarancin ruwa duk da tuba da addu’o’i, to Shari’a ta koyar da a fito gaba ɗaya domin gudanar da Sallar Roƙon Ruwa (Ṣalātul-Istisqā’), cikin ƙasƙantar da kai da nuna buƙata ga Allah Maɗaukakin Sarki.
Allah Shi ne Mai saukar da rahama. Ya ce:
﴿وَهُوَ الَّذِي يُنَزِّلُ الْغَيْثَ مِنْ بَعْدِ مَا قَنَطُوا وَيَنشُرُ رَحْمَتَهُ﴾
_”Shi ne Wanda Yake saukar da ruwan sama bayan sun yanke ƙauna, kuma Yana yaɗa rahamarSa.”_
(Suratush Shūrā: 28)
Muna roƙon Allah Ya gafarta mana zunubanmu, Ya karɓi tubanmu, Ya saukar mana da ruwan rahama mai albarka, Ya yalwata ƙasarmu da amfanin gona.
اللَّهُمَّ أَغِثْنَا، اللَّهُمَّ أَغِثْنَا، اللَّهُمَّ أَغِثْنَا. آمين.
