*KADA A RAGE ƘWAZO*
Fiye da rabin Ramadan ya riga ya wuce.
Mutane da yawa sukan fara da ƙwazo —
amma daga baya su fara kasala.
Manzon Allah ﷺ ya ce:
*أَحَبُّ الأَعْمَالِ إِلَى اللَّهِ أَدْوَمُهَا وَإِنْ قَلَّ*
_“Mafi soyuwa daga ayyuka a wurin Allah su ne waɗanda ake yi a kai a kai, ko da kaɗan ne.”_
— Sahih al-Bukhari da Sahih Muslim
Mu ci gaba da jajircewa.
Mu ci gaba da yin sallar nafila.
Mu ci gaba da ba da sadaqa da ciyarwa.
Mu ci gaba da ambaton Allah.
Ramadan bai ƙare ba tukuna.
✍️عَبْدٌ يُرِيدُ الْإِصْلَاحَ
