Shugaban Ofishin Yan Sintiri na Kano Alhaji Shehu Rabiu ya yi kira ga masu ababan hawa da su kaucewa ganganci da kasada a cewarsa ka iya jawo asarar rayuka da dukuyoyi yayin da aka shigo sabuwar shekara ta miladiyya.
Alhaji Shehu Rabiu ya bayyana haka ne yayin da yake hira da Yan jaridu a ofishinsa ya nuna bacin ransa dangane da yadda za ka ga ana tsere a unguwanni ko kuma satar hanya Inda hakan a sau tari yake jawo da na sani
Ya Kara da cewa a shekara da ta shige jami’an kungiyar sun yi namijin kokari wajen dakilewa da haura gidaje da ake yi wa mutane da Kuma sace sace da kwace kwacen wayoyi.
Shugaban kungiyar Wanda ya bayyana farin cikinsa dangane da kyakkyawar alakar da take tsakaninsu da jami’an tsaro musamman ma Yan sanda
Ya Kuma hori jami’ansa da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu ba tare da waiwayen ko kuma kallon dan abin da ake ba su ba a matsayin alawus ba bisa la”akari da muhimmanci aikin da Kuma ladan da maiduka ya yi wa maihakan tanadi ranar gobe kiyama.
Alhaji Shehu Rabiu Wanda ya Yaba da irin goyon baya da taimako da suke samu daga gwamnati Wanda ya ce Yana karfafarsu ya Kuma Yi jinjina ga daidaikun mutane irinsu Alhaji Salisu Sambajo da A A Rano da sauran makamantansu. Saboda tallafi da suke bai wa kungiyar a duk lokaci Yana mai’addu’ar kada ubangaji ya gajiyar da su.
Ya Kuma Kara kira ga sauran jama’ar gari da su yi koyi da hakan domin ganin an gudu tare an kuma tsira tare.
Kwamandan na yan Sintiri Wanda ya ce a yanzu suna da motoci wadanda suka lalace ya yi fatan za a dubi hakan da idon basirar idan aka yi la”akari da muhimmanci ababan hawa ga yan Sintiri musamman ma wajen kaiwa da komowarsu don sa Ido a kan abubuwan da suke wakana a cikin unguwanni.
Da ya juya kan babban kalubalen da suka fuskanta kuwa a kungiyance, a shekarar da aka yi bankwana da ita Alhaji Shehu Rabiu ya bayyana ta’addancin da aka yi wa wani yaronsu Inda hakan ta Kai ga rasa hannunsa a matsayin babban abin tayar da hankali a shekarar.
Alhaji Shehu Rabiu Wanda ya ce za su ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da aikinsu ya yi fatan Ubangiji ya hada kowa da alkhairan da suke cikin sabuwar shekarar ta miladiyya ya Kuma kade mugun ji da mugun gani.

